Sarakuna Ga Tinubu: Abin Ba Kyau, Ba Mu San Yadda Za Mu Lallashi Talakan Arewa Ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da alada. Kaduna Sarakunan da ke yankin Arewacin Najeriya sun yi kira zuwa ga gwamnatin tarayya kan halin kuncin da alumma ke ciki.

  • Sarakunan yankin Arewacin Najeriya sun fadakar da gwamnatin Bola Tinubu a kan halin da al’ummarsu suka shiga yanzu
  • Manyan Sarakuna sun hadu a Kaduna a karkashin jagorancin Sarkin Musulmi kuma sun ba gwamnatin Najeriya shawara
  • Mai alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar III ya ce sarakuna su ke ba talakawa hakuri, amma yanzu abin ya fi karfinsu

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna – Sarakunan da ke yankin Arewacin Najeriya sun yi kira zuwa ga gwamnatin tarayya kan halin kuncin da al’umma ke ciki.

Sarakunan Arewa a karkashin jagorancin Mai alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar III, sun ankarar da gwamnati a kan yadda ake ciki a yau.

Vanguard ta ce Sarkin Musulmi watau Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya ce sun dade su na lallashin talakawansu da su kara hakuri.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Sarkin Musulmi ya fadi masifar da za ta faru idan ba a dauki mataki ba, akwai dalilai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sultan ya ce Sarakuna, malaman addini har da gwamnonin jihohi su na cikin wadanda suka hana matasa yi wa masu mulkin kasar bore.

Amma halin da ake ciki yanzu ya yi kamari, Mai alfarma Sa’ad Abubakar III ya ce an kai yanayin da ba za a iya ba talakawa wani hakuri ba.

Mai alfarma Sarkin Musulmi ya gargadi gwamnatin tarayya cewa saboda ana ba mutane hakuri ne suka yi tsit, ba su fara juya baya ba.

Sultan yana fatan ba za a wayi gari kurum a ga talaka ya daina sauraron maganar Sarakunan gargajiya da malaman da ke Arewa ba.

Sarakunan Arewa su na ji wa Tinubu tsoro

"Mun kai matakin nan, mutane sun fusata sosai, jama’a suna cikin yunwa, sun yi fushi, amma har yanzu sun yi imani akwai masu fada masu kuma su ji."

Kara karanta wannan

Yadda Sarkin Kano Aminu Bayero Ya Saba da Sanusi II a Kan Maganar Dauke Ofisoshin CBN

"Sun yi imani da wasu gwamnoninsu, sarakunan gargajiya da wasu jagororin addini."

- Sarkin Musulmi

Idan ana zancen rashin tsaro da matsanancin talauci, Sarkin Musulmi ya ce ba za ta yiwu gwamnati ta dauka abubuwa daidai su ke ba.

Ganin halin da ake ciki ne sarakunan suka hadu a Kaduna domin ba gwamnati shawara domin ba su da wani iko a tsarin mulki.

Rashin tsaro a jihar Zamfara

A wani ƙauye da ke karamar hukumar Tsafe a Zamfara, rahoto ya zo cewa ‘yan bindiga suna ta’adi, an fi shekara 10 babu ko ‘dan sanda.

Yanzu da rana ‘yan bindiga su ke yawo cikin gidajen mutane, su na neman matansu da karfi da yaji kamar yadda mazaunan suka shaida.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllbIV5hJdmqpqqkaDCr62MoJhmrJmjwqPBjJqZoqZdl65ut9iarGaakWK6tnnSmqVmsZGZsaJ52Zpkpq1doa6tuMCsn6JlpJa5orfAsJinpaVirm6t0Z6ummWSlnw%3D

 Share!