Abubuwa 11 da Ya Dace Kowa Ya Sani a Kan Sabon Gwamnan CBN da Tinubu Zai Nada

Abuja - A yammacin Jumaa, Ajuri Ngelale ya sanar da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya zabo sababbin shugabannin bankin CBN. Rahoton nan ya kawo maku bayani game da Dr. Olayemi Micheal Cardoso wanda ake sa ran zai zama sabon gwamnan babban bankin Najeriya.

  • Idan majalisar dattawa ta tantance Dr. Olayemi Micheal Cardoso, zai zama sabon Gwamnan bankin CBN
  • Wanda aka zabo kwararren masanin tattali ne, ya rike bankuna, kamfanoni da mukamai a gwamnati
  • Cardoso ya yi aiki da kamfanonin Texaco, Chevron Oil Plc da Cities Alliance Think Tank da ke kasar waje

Abuja - A yammacin Juma’a, Ajuri Ngelale ya sanar da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya zabo sababbin shugabannin bankin CBN.

Rahoton nan ya kawo maku bayani game da Dr. Olayemi Micheal Cardoso wanda ake sa ran zai zama sabon gwamnan babban bankin Najeriya.

Punch ta tattaro tarihin masanin tattalin arzikin:

CBN: Wanene Olayemi Cardoso?

1.Olayemi Cardoso ya tashi ne a Legas, ya yi firamare da sakandare Corona School a Ikoyi da St. Gregory’s College.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sabon Gwamnan Babban Banki CBN da Mataimaka 4

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2.A jami’ar Aston da ke Amurka ya yi karatun digirin farko a ilmin shugabanci da gudanar da al’amura, ya gama a 1980.

3.Daga baya ya tafi makarantar Harvard Kennedy a kasar Massachusetts domin samun digirgir, ya kammala a shekarar 2005.

4.A 2017 jami’ar Aston da ke birnin Birmingham ta ba shi digirin digir-digir watau PhD na girmama saboda gudumuwar da ya bada.

5.A shekarar 1963, mahaifinsa watau Felix Bankole Cardoso ya zama mutumin Najeriya na farko da ya zama Akanta Janar.

6.Mista Felix Cardoso ya zama mataimakin shugaban bankin Barclays a 1972, a lokacinsa na bankin ya ca koma Union.

7.Kafin zaben shi domin ya zama gwamnan CBN, ya shafe shekaru sama da 40 ya na aiki da kamfanoni da kuma gwamnati.

8.Yayin da Bola Tinubu ya ke gwamna, shi ne Kwamishinan tsare-tsaren tattalin arziki da kuma kasafin kudi na jihar Legas.

Kara karanta wannan

Kashin Manya Da Yawa Zai Bushe da Godwin Binciken Emefiele Ya Shiga Ma’aikatu

9.Akwai lokacin da ya zama shugaban majalisar da ke kula da ayyukan gidauniyar African Venture Philanthropy Alliance.

10.Daga 2010 zuwa 2022, Cordoso ne shugaban bankin Citibank Nigeria Ltd, a shekarar da ta gabata ya ajiye wannan aiki.

11.Cordoso ya na da ‘ya ‘ya biyar da jikoki uku, asalin mahaifinsa daga Brazil su ka fito, dangin kakaninsa su na Popo Aguda.

Nadin mukamai a CBN

Ku na da labari an zabi Emem Usoro, Muhammad Sani Abdullahi, Philip Ikeazor da Bala M. Bello su zama mataimakan gwamnan CBN.

Legit.ng ta lura nadin mukamin zai karfafa jam'iyyar APC ta reshen jihar Kaduna.

Aminu Ahmad wanda aka fi sani da Abba Gadagau ya nemi takara a APC a zaben 2023, ya shaidawa Legit cewa Bola Tinubu ya dauko wanda ya cancanta.

Idan aka yi la’akari da karatunsa da aikace-aikacen da ya yi, Gadagau ya ce Muhammad Sani (Dattijo) ya cancanci ya zama mataimakin gwamnan CBN.

Kara karanta wannan

Wole Soyinka Ya Tonawa Obidient Asiri, Sun San Peter Obi Bai Doke Tinubu ba

‘Dan siyasar mai tasowa ya na ganin Dattijo zai taka rawar gani wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya, rage talauci da kawo cigaba mai dorewa a kasar.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllaoFzfY9mmJutkqrEonmQamSdmV2urm6wwJycZqOfrK5uxcBmqpqmmWKubrfAp2SsmZKku26z1pqkp5meYrCjuoydmGasmaPCo8GMsphmppGZrnA%3D

 Share!